Connect with us

News

Yan sandan Kebbi sun ceto mutum bakwai da aka yi garkuwa da su

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Rundunar ‘yan sandan Jihar Kebbi ta ce ta ceto mutum bakwai da aka yi garkuwa da su a garuruwan Bena-Mairairai da Ruwan Kanwa na jihar.

 

Advertisement

Kwamashinan ‘Yan Sanda Ahmed Magaji Kwantagora ya bayyana yayin taron manema labarai a Birnin-Kebbi cewa ‘yan fashin sun tare hanyar shiga Bena-Mairairai, inda dakarunsa suka yi wa wajen tsinke bayan samun rahoton hakan.

Jigawa: Dantata, Abdusaamad da sauran al’umma sun haɗa tallafin biliyan 1 ga waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa

Bayan fafatawa tsakanin ɓangarorin ne kuma aka yi nasarar ceto Jamila Ahamad, da Shamsiya Ahamad, da kuma Tasi’u Haruna.

Advertisement

 

A wani lamarin daban kuma, kwamashinan ya ce dakarun sun ceto wasu mutum huɗu a yankin Jega da ke jihar waɗanda su ma ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su.

Advertisement

 

Yayin samamen, ‘yan sanda sun ƙwace mota ƙirar Toyota Corolla daga hannun ‘yan fashin, “sannan an tsaurara sintiri don hana mahara sakat a yankin,” in ji shi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending