Connect with us

News

Sojoji 122 Sun Samu Karin Girma Zuwa Matsayin Janar

Published

on

Babban Hafsan Sojojin Kasa, Laftanar Janar Faruk Yahaya

DAGA MARYAM BASHIR MUSA

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya ta yi wa hafsoshinta 122 karin girma zuwa matsayin Manjo-Janar da kuma Birgediya-Janar.

 

Advertisement

Hafsoshin sojin da suka samu karin girman sun hada da Birgediya-Janar 52 da aka daga likafarsu zuwa Manjo-Janar sai kuma Kanar-Kanar 70 da suka samu karin girma zuwa Birgediya-Janar.

Ghana ta nuna tsoro kan sojojin hayar Rasha da Burkina Faso ta dauko

 

Advertisement

Sanarwar da Daraktan Yada Labarai na rundunar, Birgediya-Janar Onyema Nwachukwu, ya fitar a safiyar Juma’a ta ce hafsohin sun samu karin girma ne saboda aiki da suka yi wurjanjam domin kare kasa.

 

Advertisement

Da yake taya su murna, Babban Hafsan Sojin Kasa na Najeriya, Laftanar-Janar Faruk Yahaya, ya ce sabuwar amanar da aka ba su na bukatar su kara jajircewa da sadaukarwa da kuma biyayya ga Najeriya da kuma kare hadin kanta.

 

Advertisement

 

Daga cikin wadanda suka samu karin girma zuwa mastayin Manjo-Janar har da Birgediya-Janar AA Ayanuga na Sashen Sufuri da Kirkira na rundunar da EH Akpan na Rundunar Operation Hadin Kai da NM Jega da ke Hedikwatar Tsaro da JO Ugwuoke na Sashen Jigila na rundunar.

Advertisement

Sauran sun hada da PAO Okoye na Sashen Ayyuka da EF Oyinlola na Sashen Ayyuka da Shirye-shirye na Musamman da AE Edet na Makaranar Aikin Injiniya da AB Mohammed Hedikwatar Rundunar a Sashen Sanya Ido da kuma MT Usman na Rundunar Tsaron Shugaban Kasa.

 

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending