News
Kotu Ta Tsare Wata Mata Kan Zargin Kashe ‘Yar Aikinta
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Wata babbar kotu da ke Jos a Jihar Filato, ta bayar da umarnin tsare wata matar aure, Nneamaka Nwachuku, bisa zargin laifin azabtar da ‘yar aikinta mai shekaru 11, Margret Joshua wadda ta mutu har lahira.
Magoya byan Moroko na sa ran matsayi na uku a World Cup
Alkalin kotun, B. Bassi, wanda ya jagoranci shari’ar, ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare wadda ake tuhumar a ranar Laraba.kamar yanda jaridar leadship ta rawaito
An ce matar ta gallaza mata azaba wanda hakan ya sa ta mutu har lahira a ranar 11 ga watan Nuwamba.
‘Yansandan sun tuhume ta da laifuka guda uku na kisan kai, azabtarwa da kuma haifar da rauni.
Rundunar ‘yansandan ta ce Mista Nwachukwu, da ke karamar hukumar Jos ta Kudu a Jihar Filato, ta yi amfani da man gyada mai zafi ta zuba wa ‘yar aikin a sassan jiki.
‘Yansanda sun ce “ta ci gaba da gana mata azaba har sai da ta kai ga mutuwarta.”
Kotun ta dage ci gaba da sauraren karar zuwa ranar 19 ga watan Janairun 2023, domin masu gabatar da kara su tabbatar da karar.
-
News2 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion6 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News2 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
