Connect with us

News

Bala’in sanyi ya sa mutane sun kasa fita daga motocinsu a Amurka

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Akalla mutum 28 sun mutu a Jihar New York yawancinsu a garin Buffalo, a yayin da mahaukaciyar iska mai dauke da jaura take ci gaba da mamaye Arewacin Amurka.

 

Advertisement

Wani jami’in gwamnatin jihar ya ce lamarin ya rutsa da mutane da dama inda wasu suka kwashe fiye da kwana biyu a cikin motocinsu a yanayin iskar sanyi mafi muni a tarihi.

Liverpool Ta Sayi Cody Gakpo Daga PSV

Advertisement

Kankarar da ke sauka ta kai santi mita 23, kamar yadda masana suka yi hasashe.

 

Advertisement

Mahaukaciyar iskar mai bala’in sanyi ta somo ne daga Canada zuwa kan iyakar Mexico inda ta kashe akalla mutum 56.

 

Advertisement

Shugaban Amurka Joe Biden ya ayyana dokar ta-baci inda ya amince a bayar da tallafi na musamman ga jihar New York.

 

Advertisement

“Ina jajanta wa mutanen da suka yi asarar ‘yan uwansu a wannan lokaci da ake hutun karshen shekara,” in ji shugaban kasar a wani sako da ya wallafa a Tuwita.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending