News
An gano gawar mutum 25 da matsanancin sanyi ya kashe a New York din Amurka
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Tawagar agajin gaggawa a yammacin jihar New York a Amurka sun gano gawarwakin mutum 25 da suka mutu sakamakon mummunan matsanancin sanyi da dusar ƙanƙara a ƙarshen makon nan.
Galibinsu sun sun mutu ne a cikin a birnin Buffalo da kewayensa.
Sojoji uku sun mutu bayan da jirginsu ya kama da wuta a Nijar
An sake yin hasashen samun ƙarin dusar ƙanƙara a can, yayin da dokar hana tuƙi ke ci gaba da aiki.
Shugaban yankin Erie — wanda ya hada da Buffalo — ya ce watakila wannan ne yanayi mafi muni da aka fuskanta a tarihin birnin.
Jami’an tsaron ƙasar sun kuɓutar da ɗaruruwan mutanen da suka maƙale a cikin motoci da a gidajen da ba su da wutar lantarki.
Matsanancin sanyin da dusar ƙanƙara da aka gani ya yi sanadin mutuwar mutum kusan 50 a arewa maso gabashin Amurka
