Connect with us

News

Masu garkuwa sun kashe wasu ‘yan gida ɗaya bayan sun karɓi fansar naira miliyan 60

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

 

 

Masu garkuwa da mutane sun kashe wasu ‘yan uwan juna su uku tare da wani mai babur bayan da suka karɓi fansar naira miliyan 60 daga mahaifin yaran a jihar Taraba da ke arewa maso gabashin Najeriya.

 

Advertisement

Jaridar daily Trust a Najeriya ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a kusa da dajin Garin Dogo a yankin ƙaramar hukumar Lau ranar Lahadi.

Sojoji uku sun mutu bayan da jirginsu ya kama da wuta a Nijar

Rahotonni sun ruwaito cewa masu garkuwar sun kama mutanen uku – waɗanda suke uwa ɗaya uba ɗaya – inda kuma suka buƙaci naira miliyan 100 a matsayin kuɗin fansa.

 

Mahaifin yaran uku wanda mai sana’ar safarar shanu ne ya daidaita da masu garkuwar – waɗanda suka amince zai biya su naira miliyan 60 domin sakin ‘ya’yan nasa uku.

 

Sai kuma ya ɗauki ɗan achaba tare da bashi kuɗin domin kai wa masu garkuwar a cikin dajin da ke kusa da ƙauyen nasu, dan sakin ‘ya’yan nasa .

Advertisement

 

To sai dai bayan kai kuɗin fansar da mai babur ɗin ya yi sai suka kashe shi tare da sauran yaran uku, bayan sun karɓi kudin fansar.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending