Sports
Chelsea ta ɗauki Malo Gusto daga Lyon
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Chelsea ta ɗauki ɗan wasan bayan Faransa Malo Gusto daga Lyon kan kuɗi fam miliyan 30.7
Gusto mai shekara 19 ya sanya hannun kan kwantiragi da Chelsea har zuwa kakar wasa ta 2030.
A wata sanarwa da Chelsea ta fitar, ta ce matashin ɗan ƙwallon zai ci gaba da taka-leda a Lyon har zuwa ƙarshen kakar wasa ta bana kafin ya fara wasaa ƙungiyar a sabuwar kakar wasa mai zuwa.
Gusto ya fara buga wa Lyon wasa ne a watan Janairun 2021, inda kawo yanzu ya buga wa ƙungiyar – wadda ke mataki na tara a kan teburin Ligue 1 – wasa 15
Kawo yanzu Chelsea ta sayi ‘yan wasa shida a cikin Janairun da muke ciki, bayan karɓo aron Joao Felix daga Atletico Madrid.
Advertisements
