News
Akpabio Ya Yi Suɓul-da-baka Kan ‘Kuɗaɗen More Hutun’ Sanatoci
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.
Shugaban Majalisar Datawan, Godswill Akpabio ya yi suɓul-da-baka, inda ya sanar da cewa majalisar ta tura wa mambobinta ‘kuɗin more hutu’.
A lokacin zaman majalisar na ƙarshe kafin tafiya hutu, Akpabio ya ce “Da zarar an rantsar da Sanata Umahi a matsayin minista, za mu sake tsara shugabancin majalisar.”
Sai ya ce “Domin more hutunmu, Akawun majalisa ya tura ɗan wani abu a asusun ajiyar kowannenmu.”
Bayan ya yi furucin ne ɗaya daga cikin ƴan majalisar ya matsa kusa da shi, don fargar da shi cewa ana nuna zaman nasu kai-tsaye ta talabijin.
Daga nan ne sai Akpabio ya yi saurin warware maganar tasa, inda ya ce “Na janye kalaman da na yi. Ina nufin shugaban majalisa ya tura maku addu’ar fatan shan hutu lafiya da kuma fatan yin tafiya lafiya a dawo lafiya.”
Babu dai tabbacin game da adadin abin da aka tura wa ƴan majalisar, musamman ma yadda albashinsu da kuma sauran kuɗaɗen alawus ɗinsu duk abubuwa ne da babu hakiƙanin bayani a kai.
An yi ta yamaɗiɗi da bidiyon a shafin Tuwaita, wanda ke nuna shugaban majalisar yana bayani game da alawus ɗin hutun, da ta ce Godswill Akpabio ya yi suɓul-da-baka wajen furtawa a daidai lokacin da ‘yan Najeriya ke fama da matsin rayuwa.