Connect with us

News

Yadda noman rani ya zama mafita akan karancin abinci a kasar nan

Published

on

noman rani
Spread the love

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Wannan na faruwa ne a daidai lokacin da ake samun hauhawar farashin kayan abinci, wanda ya yi tashin da ba a taba ganin irinsa ba a cikin shekara kusan 20, kamar yadda alkaluman Hukumar Kididdiga ta Kasar (NBS) suka bayyana.

Advertisement

‘Yan Nijeriya da dama ba sa iya ciyar da iyalinsu yadda ya kamata. Damuwarsu ita ce farashin kayan ya ki saukowa duk da cewa ana tunkarar karshen damina, a daidai lokacin da sabon amfanin gona yake isa kasuwa wanda hakan ke taimakawa wajen sauko da farashi.

Tinubu ya mayar da martani kan juyin mulkin da aka yi a Gabon.

Tsoron kada a ci gaba da tashin kayan abincin ya sa gwamnatin Nijeriya ayyana dokar ta-baci inda ta fito da wasu tsare-tsare – na nan-take da na matsakaicin lokaci da kuma na dogon lokaci don magance matsalar.

Galibi ana noma a kasar nan  daga lokaci zuwa lokaci, kuma an fi yin aikin gona ne a lokacin damina.

Advertisement

Kashi 90 cikin 100 na aikin gonar da ake yi a kasar ya dogara ne da damina, kamar yadda Bankin Ci-gaban Afirka ya bayyana ta hannun shirin Country Food and Agriculture Delivery Compact.

Alkaluman sun nuna cewa kaso 10 cikin 100 na manoman Nijeriya ne suke noman rani kuma su ne nauyin ciyar da kasar da ta fi kowace yawan jama’a ya rataya a wuyansu bayan damina ta tafi.

“Shugaban kasa ya ce ba za mu lamunci aikin noma na lokaci zuwa lokaci ba. Ba za mu lamunci karancin abinci ba,” kamar yadda Alake ya bayyana yayin ayyana dokar ta-bacin.

Advertisement

Ana bayar da shawarar sanya duka wasu muhimman abubuwa a jerin kayan da Majalisar Tsaro ta Kasar (National Security Council) za ta sanya ido a kansu.

Alake ya kuma bukaci hadin gwiwa tsakanin Ma’aikatar Aikin Gona da Ma’aikatar Albarkatun Ruwa don tabbatar da wadatuwar kasar noman da za a rika yin noma a duk tsawon shekara.

Nijeriya tana da yalwataccen ruwa da za a iya noma da shi a gaba daya kasar, ciki har da manyan koguna 12 wadanda suke da wadataccen ruwa da za iya aikin noman rani a kasar noman da ta kai girman hekta miliyan 3.14.

Advertisement

A zahiri karamin bangare daga cikin makeken filin kasar noman kasar ne aka yi masa tsarin aikin noman rani.

“Kamar yadda majiyoyi da dama suka bayyana, filin kasar noman hekta 400,000 ne aka yi masa tsarin aikin noman rani a Nijeriya,” in ji Farfesa Abba Aminu, babban darakta aikin gona a hukumar kula da kogunan Hadejia da Jama’are.

Ko da yake wasu suna ganin adadin bai kai haka ba, inda suke cewa kasar da aka yi wa tsarin noman rani ba ta wuce hekta 100,000 idan aka kwatanta da hekta miliyan uku da ake bukata.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *