Connect with us

News

Abinda Da Zai Kawo Karshen Juyin Mulkin Sojoji A Nahiyar Afirika–Shehu Sani

Published

on

Sanata Shehu Sani

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

Tsohon dan majalisa kuma fitaccen mai sukar lamirin gwamnatin Najeriya, Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa magudin zabe  ne ke haddasa rugujewar dimokuradiyya a Afirka.

Advertisement

Kalaman Sani na zuwa ne a daidai lokacin da aka yi juyin mulki a kasar Gabon dake Afirka ta Tsakiya.

Yadda noman rani ya zama mafita akan karancin abinci a kasar nan

Jaridar Indaranka  ta rawaito cewa da sanyin safiyar yau ne jami’an soji a Gabon suka sanar da kwace mulki bayan sake zaben shugaba Ali Bongo Ondimba a karo na uku.

Advertisement

Rahotanni sun ruwaito cewa manyan hafsoshin sojin kasar ne suka bayyana hakan a ranar Talata a babban gidan talabijin na kasar.

An bayar da rahoton cewa, jami’an sun sanar da soke sakamakon zaben na ranar Asabar da ‘yan adawa suka yi watsi da su tare da bayyana shi a matsayin zaben shugaban kasa mai cike da magudi.

Advertisement

Sai dai Sani, a wani sako da ya wallafa ta dandalinshi na sada zumunta na X, ya zargi iyalan Bongo da mamayar da ruguza dimokradiyya a Gabon.

Ya rubuta cewa mutane a Gabon sun fito suna yin zanga-zanga kan tituna don nuna goyon bayan juyin mulkin da aka yi a Libreville. Iyalan Bongo sun mamaye kuma sun ruguza Dimokradiyya. Dimokuradiyya na mutuwa a Afirka muddin anayin zabe mai cike da magudi.

Advertisement

Kuma muddin idan har za’a cigaba da yin murdiya wajen gudanar da zabe a kasashen Afirika to ba za’a daina ganin sojoji na karbe mulki daga hannun zababbun shugabannin kasashe ba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending