News
An Hana Mataimakin Gwamnan Jahar Edo Shiga Ofishinsa
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Gwamnan jihar Edo, Comrade Philip Shaibu, shiga ofishinsa da ke Dennis Osadebey Avenue, wato fadar gwamnatin jihar da ke birnin Benin, babban birnin Jihar Edo.
Wannan wani abu ne da ke nuna yadda dangantaka ta ƙara tsami a tsakanin Gwamnan Jihar Edo Andrew Obaseki da mataimakin nasa, Shaibu.
Kungiyar Kwadago Na Shirin Tsunduma Wani Sabon Yajin Aiki Mai Dogon Zango
Shaibu wanda ya tafi ofis da niyyar shiga domin gudanar da ayyuka kwatsam sai ya tarar da an kulle kofar shiga.
Mataimakin gwamnan da hadimansa sun shafe tsawon awa guda suna tunanin ko daga baya za a bude musu kofar ofishin amma hakan ya ci tura daga bisani dole suka juya.
Shaibu ya yi ta kiran Gwamnan jihar Andrew Obaseki a wayar salula amma bai samu damar magana da shu ba.
Majiyoyi sun shaida cewar Shaibu ya yi magana da kwamishinan ‘yansandan jihar da daraktan ‘yansandan ciki na (DSS) inda ya shaida musu yadda aka kulle masa ofis da hanasa shiga.
Mataimakin Gwamnan ya kira kwamandan tsaron gidan gwamnatin jihar SP Ibrahim Babatunde, inda ya tambaye shi da dalili hana shi shiga ofishinsa, sai ya amsa da cewa umarni ne daga sama. Ya kara da cewa babban jami’in tsaron Gwamna (CSO) Wabba Williams, shi ne ya fi kamata a nemo domin ya yi bayanin da ya dace.
Shaibu ya kira Williams inda ya yi alkawarin cewa yana zuwa amma har tsawon lokacin da mataimakin gwamnan ya shafe yana jira bai zo ba.
“Har zuwa yanzu, ban samu wata sanarwa a hukumance kan inda zan koma ba. Illa wadanda suke da bayanin su ne ma’aikatana. Ma’aikatan gwamnati na da bayanin a hukumance amma ni ba ni da shi. A daidai lokacin nan da nake magana da kai, ina tsaye a mashigar gidan gwamnatin,” Shaibu ya shaida a lokacin da aka jiyo shi yana waya da wani mutum da ba a gane waye ba.
A makon jiya, an ce a wata wasika daga ofishin shugaban ma’aikatan jihar, Anthony Okungbowa, da aka aike ga babban sakataren ofishin mataimakin Gwamnan, ta unarci Shaibu da ya koma sabon ofishinsa da ke lamba 7 Dennis Osadebey Avenue, GRA, a birnin Benin babban fadar jihar.
LEADERSHIP ta labarto cewa makonni biyu da suka gabata an hango alamin ofishin mataimakin gwamnan a wani sabon ofishi da ake son ya koma da ke da tazarar mitoci da fadar gwamnatin jihar, sai dai Shaibu ya nace kan cewa ba a sanar da shi cewa za a canza masa ofishi da fitar da shi daga fadar gwamnatin ba.
Wani labarin kuma Wani bawan Allah ya Gwnagwaje Auwalu Salihu da Sabon Adaidaita Sahu.
A yayin da ake cigaba da samun cikas wajen balaguro a filin jirgin sama na Murtala Muhammed dake Legas, biyo bayan komawar da kamfanonin jiragen sama na kasashen waje suka yi zuwa sabuwar tashar jiragen sama, gwamnatin tarayya ta gayyaci kamfanonin jiragen sama na kasashen waje zuwa wani taro a yau.
A sakamakon haka, kwamitin da ministan harkokin sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya kafa domin duba rudanin tafiye-tafiye a filin jirgin sama naMurtala Muhammad da kwamitin ministoci zai gana da masu ruwa da tsaki a domin nemo bakin zaren da warware matsalar.
Fasinjojin kasa da kasa da suka tashi daga Najeriya a ranakun Laraba da Alhamis sun makale a biranen Legas da Cairo da Doha da Landan, da sauran wurare bayan da madaurin kaya na jirgi ya lalace a sabon filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas, al’amarin da ya tilastawa kamfanonin jiragen sama jinkirtawa tare da soke tashin jirage.
Har yanzu zuwa karshen mako matsalar tafiye-tafiye na ci gaba da wanzuwa inda fasinjojin ke kwashe sa’o’i a kan layi domin tantance su ta hanyar binciken tsaro
