News
Kisan Edo: Jami’an Hukumar DSS Sun Kama Manyan Mutane Biyu Da Ake Zargi
Jami’an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) sun cafke wasu manyan mutane biyu da ake zargi da hannu wajen kisan matafiya 16 da aka yi a Uromi, karamar hukumar Esan Arewa maso Gabas ta jihar Edo a makon jiya.
Sanarwar da Babban Sakataren Yada Labarai na gwamnan jihar, Friday Ituah, ya fitar a ranar Talata ta tabbatar da kamen, inda ya ce an kama su ne bisa sahihan bayanan sirri.
Shugaba Tinubu Ya Sauke Mele Kyari, Ya Naɗa Bashir Ojulari a Matsayin Sabon Shugaban NNPC
A cewarsa, jami’an tsaro na ci gaba da farautar wasu da ake kyautata zaton suna da alaka da wannan aika-aika. Hukumomin tsaro sun garzaya da wadanda aka kama zuwa Abuja don ci gaba da bincike da shirin gurfanar da su a gaban shari’a.
A ranar Litinin, Gwamnan Edo, Sanata Monday Okpebholo, ya kai ziyarar jaje jihar Kano ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu. Ya bayyana cewa an kama mutum 14 da ake zargi da hannu a lamarin, kuma dukkansu za a kai Abuja don karin bincike.
Gwamnan ya tabbatar wa iyalan wadanda abin ya shafa cewa gwamnati za ta tabbatar da adalci, tare da biyan diyya ga iyalan da suka rasa ‘yan uwansu.
-
News19 hours ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
-
News1 day ago
Ana Zargin Matar Aure Da Shaƙe ’Yar Kishiyarta Mai Shekara 3 Har Lahira
-
News6 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
