News
Kungiyar Who Is Fixing The North? Ta Jinjinawa Gwamnan Edo Kan Dakatar Da ’Yan Banga Da Jajantawa Kanawa
Kungiyar Who Is Fixing The North? ta yabawa gwamnan jihar Edo, Sanata Monday Okpebholo, bisa daukar matakan gaggawa biyo bayan kisan gillar da wasu matafiya suka fuskanta a garin Uromi, jihar Edo, a ranar 27 ga Maris, 2025.
Sanarwar da shugaban kungiyar, Mustapha Dawood (Sir Sa’e), ya fitar ta bayyana gamsuwa da yadda gwamnan ya jajantawa iyalan wadanda abin ya shafa a jihar Kano, tare da tabbatar musu da cewa za a yi adalci.
Baya ga haka, Gwamna Okpebholo ya sanar da dakatar da dukkan kungiyoyin ‘yan banga a jihar Edo nan take, da kuma dakatar da kwamandan ‘yan sanda na jihar, CP Friday Ibadin (mai ritaya), bayan bayyanar rahotannin da ke nuna cewa wasu ‘yan banga sun aikata kisan gillar ba tare da bin doka ba.
Kungiyar ta bayyana cewa matakin gwamnan na tabbatar da doka da oda ya nuna jajircewar sa wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a. Haka kuma, ta jinjinawa hadin gwiwar gwamnatocin Edo da Kano, tare da bayyana hakan a matsayin misali na jagoranci na gari da ke nuna muhimmancin hadin kai da tausayi a lokacin bala’i.
A karshe, kungiyar ta yabawa mutanen Uromi da suka nuna jarunta wajen ceto wasu daga cikin wadanda lamarin ya shafa, tana mai jaddada cewa adalci zai yi aiki domin hukunta masu hannu cikin wannan danyen aiki.
-
News1 day ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
-
News2 days ago
Ana Zargin Matar Aure Da Shaƙe ’Yar Kishiyarta Mai Shekara 3 Har Lahira
-
News7 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
