News
NIMC Ta Yi Wa Mutane Miliyan 117 Rijista A Najeriya
Hukumar yi wa ‘yan kasa rijista ta Najeriya (NIMC) ta bayyana cewa ta yi wa fiye da mutane miliyan 117 rijista zuwa karshen watan Fabrairu da ya gabata.
Rahoton hukumar ya nuna cewa Jihar Kano ke kan gaba da kaso 56.5, wanda ya kai mutane miliyan 66,281,803. A daya bangaren kuma, mata miliyan 51,079,521 ne aka yi wa rijista, wanda ke wakiltar kaso 43.5.
Allah Ya Yiwa Galadiman Kano Alh Abbas Sunusi Bayero Rasuwa.
Jihar Legas ce ta fi kowacce jiha yawan rijista, inda sama da mutane miliyan 12.6 suka yi rijista. Kano na biye mata da mutane sama da miliyan goma.
A daya bangaren kuma, jihohin Ekiti, Bayelsa da Ebonyi su ne ke da mafi karancin adadin rijista. A Bayelsa da Ebonyi, mutane kasa da miliyan daya ne suka yi rijista, yayin da a Jihar Ekiti, mutane miliyan daya da dubu dari daya ne suka yi rijista.
Hukumar ta NIMC na ci gaba da kokarin tabbatar da cewa dukkan ‘yan Najeriya sun samu rijista don mallakar lambar shaidar dan kasa.
