News
Kotun sauraren kararrakin zabe da ke jihar Kaduna, ta bayyana zaben Sanata Uba Sani a matsayin “Inconclusive”
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Kotun sauraren kararrakin zabe da ke zamanta a Kaduna, jihar Kaduna, ta bayyana zaben Sanata Uba Sani na jam’iyyar APC a matsayin wanda bai kammala ba.
Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da dan takararta, Isah Mohammed Ashiru sun shigar da kara suna kalubalantar nasarar Uba Sani.
Gwamnatin Tarayya Ta Yi Tir Da Yadda Gwamnatin Zamfara Ke Siyasantar da Harkar Tsaro.
Kwamitin mai mutane uku karkashin jagorancin mai shari’a Victor Oviawe ya kuma bayar da umarnin sake gudanar da zabe a unguwanni bakwai, kananan hukumomi hudu, rumfunan zabe 24 da suka kunshi masu rajista 16,300.