News
Sama Da Mutane 4,000 Sun Si Rajista Da Shirin Auren Zawarawa A Jahar Kano
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Hakumar Hisbah a jihar Kano sama da mutane dubu 4 ne suka yi regista da shirin auren zawarawa da gwamnatin jihar ta shirya yi wata mai kamawa.
Hisbah tace tayi nasarar tantance mutane dubu 1,800 da zata hada aure, kuma tuni ta tsara tantance duba lafiyar ma’auratan wanda ya zama wajibi gabanin shirye-shiryen shagulgulan bikin.
Sama Da Mutane 4,000 Sun Si Rajista Da Shirin Auren Zawarawa A Jahar Kano
Da yake jawabi ga manema labari mataimakin babban kwamandan hakumar Mujahid Aminuddeen, ya bayyana cewa, wadanda aka tantance zasu halarci gwajin kwayar cutar HIV da kwayar halitta ta Genotype da gwajin kwayoyi gabanin daurin auren.
Mujahid yace gwamnatin jihar ta kuduri aniyar hada aurarraki 1,800 a rukunin farko, yayin da sama da mutane dubu 4000 suka yi regista.
Mallam Mujahid ya kara da cewa lura za matsin tattalin arziki da ake fama da shi a fadin kasa, mutane da dama suna fatab kasancewa cikin shirin musamman yammata da zawarawa wanda suka fito daga gidajen masu karamin karfi.
Sai dai ya shawarci wadanda suka ci gajiyar shirin auren da su zauna, lafiya da aminci da juna, inda yayi gargadin cewa duk wadanda suka kashe aurensu ba tare da kwakkwaran dalili ba zasu biya gwamnatin jihar kudaden da ta kashe.
-
News7 days ago
Magoya Bayan APC Sun Yi Allah-Wadai da Rushe Gidan Sani Sha’aban, Sun Buƙaci a Yi Adalci
-
News6 days ago
Ƙungiyar ’Yan Kasuwar Wayoyi Ta Buƙaci NCC Ta Dakatar Da Tsarin Tantance Wayoyi Na DMS Tsawon Kwanaki 90
-
News7 days ago
Musa Illiyasu Kwankwaso Ya Taya Sanata Lado Murnar Cika Shekaru 60, Ya Kira Shi Gogaggen Ɗan Siyasa

