News
Yajin aiki: Tinubu ya Gayyaci Kungiyar Ƙwadago ta NLC da TUC
Daga Yasir Sani Abdullahi
Shugaban kasa Bola Tinubu ya Gayyaci shugabannin kungiyoyin kwadagon Nigeria wadanda suka haɗa na NLC da TUC, a kokarin sa na dakile yajin aikin da suke shirin tsunduma a ranar talata 03 ga watan October.
Indaranka ta rawaito cewa Shugaban kasar zai gana da Shugabannin yan ƙwadago da misalin karfe 2 na ranar lahadin nan a fadar shugaban kasa Aso Rock Villa.
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito tun a makon da ya gabata kungiyoyin kwadagon suka bada sanarwar fara yajin aikin sai baba-ta-gani , sakamakon gazawar gwamnatin tarayya wajen cika alkawuran da ta dauka na shawo kan tarin matsalolin da yan Nigeria suke fuskanta tun bayan janye tallafin man fetur.