Connect with us

News

Cece Kucen Mutane Ba Zai Sa Mu Yi Abinda Ba Shi Bane Ba-Alkalin Alkalai

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

A karshe babban alkalin alkalan Najeriya, Olukayode Ariwoola, ya mayar da martani kan zarge-zargen nuna son kai a kan batutuwan da suka shafi zaben 2023.

Jaridar DAILY POST ta rawaito cewa kotunan zabe da kotun daukaka kara sun soke zabukan da aka yi na masu rike da mukaman gwamnati da aka zaba a babban zaben da ya gabata.

Gwamnan Kano Abba Kabir ya nada sabon shugaban ma’aikatan jihar

Kotu ta kori wasu gwamnoni da Sanatoci da ‘yan Majalisar Wakilai saboda korafin da jam’iyyun adawa suka yi.

 

Advertisement

Magoya bayan shugabannin da aka kora dai sun zargi bangaren shari’a da goyon bayan jam’iyyar All Progressives Congress, APC.

 

Sai dai da yake magana a wajen bude zama na musamman na shekarar shari’a ta 2023/2024 da kuma rantsar da sabbin manyan lauyoyin Najeriya 58, Ariwoola ya bukaci alkalai da su tsaya tsayin daka, yana mai cewa bai kamata a ruguza tunanin shari’a ba.

 

Ya roƙi alƙalai da kada su damu da ra’ayin ‘yan tawayen yayin da suke yanke shawara a kan batutuwa.

 

Advertisement

Ya ce,har yanzu ya zama dole a yi la’akari da cewa ra’ayin jama’a, ba zai sa ku kauce daga kasancewa a matsayin doka ba wajen yanke hukunci kan shari’o’in da ke gaban ku.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending