Connect with us

News

Gwamnan Kano Abba Kabir ya nada sabon shugaban ma’aikatan jihar

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

Gwamnan jihar kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince da nada Alhaji Abdullahi Musa a matsayin sabon shugaban ma’aikatan gwamnatin jihar

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban Sakataren yada labaran gwamnan Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa da Jaridar Inda Ranka

KASSOSA ta zabi sabbin shugabannin da za su rike kungiyar

Yace nadin nasu na zuwa ne bayan da tsohon shugaban ma’aikatan jihar kano Usman Bala ya kammala aikin sa , Inda yayi ritaya daga aikin gwamnati tun a watan mayun shekara ta 2023, kamar yadda doka ta tanada .

Sanarwar ta ce Alhaji Abdullahi Musa kwararen ma’aikacin gwamnati ne da yayi aiki a hukumomi da ma’aikatun gwamnatin jihar kano, kuma haifaffen karamar hukumar Kiru ne.

Abdullahi Musa ya taba zama babban Sakatare a gidan gwamnatin jihar kano da majalisar zartarwa ta jihar da kuma ma’aikatar aiyuka na musamman da dai sauransu.

Advertisement

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya bukaci sabon shugaban ma’aikatan da ya gudanar da aikin sa cikin kwarewa da bin dokoki da ka’idojin aikin gwamnati

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending