Connect with us

News

KASSOSA ta zabi sabbin shugabannin da za su rike kungiyar

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Kungiyar tsofaffin daliban kwalejojin kimiyya ta jihar Kano (KASSOSA), ta zabi sabbin shugabannin da za su tafiyar da harkokin kungiyar nan da shekaru uku masu zuwa, wanda aka gudanar a Jami’ar Yusuf Maitama Sule Kano.

Da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala zaben, shugaban kwamitin zaben Farfesa Balarabe Sarki Sagagi ya ce shirya zaben ya zama wajibi saboda wa’adin tsoffin shugabannin kungiyar ya zo karshe.

Gwamnatin Kano za ta Inganta Bangaren Sashin Samar Da Magungunan Jihar

Farfesa Sarki Sagagi ya ci gaba da cewa kwamitin amintattu na KASSOSA ya dauki gabarar shirya zaben ne domin baiwa ‘ya’yan kungiyar damar hidintawa kungiyar don cimma manufofin kafata.

 

Advertisement

“Kamar yadda kuke gani, mun gudanar da wannan zaben ne domin baiwa sauran mambobinmu damar kada kuri’a ga ‘yan takarar da suka fito mukamai daban-daban,” in ji Farfesa Balarabe Sarki Sagagi.

 

Da yake jawabi tun da fari, zababben shugaban kungiyar KASSOSA Malam Balarabe Nuhu Jalla Dambatta, dan ajin Kwalejin Kimiyya ta Dawakin Kudu shekarar 1989, ya yi alkawarin tafiya da kowa ba tare da nuna wariya ba.

 

Sabon Shugaban ya jaddada kudirinsa na ci gaba da kyawawan manufofin inganta kwalejojin kimiyya, da ma ciyar da tsoffin dalibai gaba.

 

Advertisement

 

Jalla ya ce a cikin shekaru uku da suka gabata, kungiyar KASSOSA ta kasa ta kashe miliyoyin Naira wajen tallafawa mambobinsu domin dogaro da kai karkashin shirin ‘uwar kungiyar ta KASSOSA na koyar da sana’o’i.

 

“Baya ga wannan shirin da ya taba zukatan ‘yan kungiyar KASSOSA da dama, musamman matasa a cikinmu, mun kuma gyara dakunan gwaje-gwaje, ajujuwa, da sauran gine-gine a wasu kwalejojin Kimiyya dake fadin jihar Kano” a cewar Balarabe Jalla.

 

Daga nan sai ya yi kira ga sauran mambonin KASSOSA na Kano da Jigawa da su ci gaba da ba da tasu gudunmawar domin farfado da martabar kwalejojin.

Advertisement

 

Sabbin zababbun shugabannin KASSOSA sune:

 

· Balarabe Nuhu Jalla, ya zama shugaban kasa da kuri’u 390

 

· Abubakar Ado Gwaram, mataimakin shugaban kasa (I), da kuri’u 388

Advertisement

 

 

· Mabruka Abubakar a matsayin mataimakin shugaban kasa (II), da kuri’u 377

 

· Kabir D. Kabir, Babban Sakatare, da kuri’u 359

 

Advertisement

· Abubakar A. Yakasai, Mataimakin Sakatare Janar, da kuri’u 368

 

 

 

· Salisu Mustapha sakataren kudi ya samu kuri’u 134

 

Advertisement

· Aisha Kasim – Sakatariyar kudi, 267 kuri’u

 

· Jamilu L. Abdullahi, Ma’aji yana da kuri’u 195

 

· Umar A. Rabo, Ma’aji da kuri’u 199

 

Advertisement

Bashir B. Roba, a matsayin Auditor na cikin gida da kuri’u 344

 

· Halliru Sani, Jami’in Hulda da Jama’a (I) ya samu kuri’u 341

 

 

· Abba T. Ibrahim Jami’in Hulda da Jama’a (II) da kuri’u 353

Advertisement

 

· Engr. Mustapha Aminu, Sakataren Ilimi yana da kuri’u 205

 

· Maryam U. Usman, mai ba da shawara kan harkokin shari’a ta samu kuri’u 290 kuma

 

 

Advertisement

· Binta I. Waziri, a matsayin jami’ar jin dadin jama’a da kuri’u 368

 

Ta cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na kungiyar ya fitar, Halliru Sani, ya ce KASSOSA ba za tayi kasa a gwiwa ba, wajen ci gaba da tallafawa mambobinta a duk inda suke.

 

Ya kuma tabbatar wa da sauran ‘yan kungiyar cewa sabbin shugabannin za suyi duk mai yiwuwa wajen ganin ‘ya’yan kungiyar sun ci gaba da alfahari da ita.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending