Connect with us

News

Mai Gonar Tabar Wiwi A Sakkwato Ya Yi Murna Da Hukumar NDLEA Ta Kama Shi

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

 

Advertisement

Mai gonar tabar wiwi ’yar kasar waje ta farko a Jihar Sakkwato ya ce ya yi farin ciki da hukuma ta kama shi.

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NLEA) ta kama shi ne bayan ta gano gonar tasa a yanki Sanyinna da ke Karamar Hukumar Tambuwal.

Advertisement

Shugaban kamfanin BUA Abdul Samad ya ki karbar mukamin da APC ta ba shi

Kwamandan NDLEA na jihar, Iro Adamu, ya ce, wanda ake zargin “ya shuka tabar wiwin ne a cikin masara kuma babu wanda zai gane sai kwararre.

“Tabar wiwin da ya shuka ta kasar waje ce kuma tana da tsada sosai,” in ji shi.

Advertisement

Ya ce karon farko ke nan ta aka gano gonar tabar wiwi a Jihar Sakkwato don haka akwai bukatar wayar da kai da kuma sintiri don hana al’umma wannan muguwar sana’a.

Aminiya ta ruwaito cewa Magidancin da ake zargin ya ce a Legas ya gano sana’ar, shi ne da ya dawo gida ya nemi ya fara.

Advertisement

“Karon farko ke nan, kuma na koyi harkar ce a Legas, da na dawo Sanyinna kuma na nemi in jaraba.

“Yayana ya yi kokarin hana ni, amma na ki ji.

Advertisement

“Amma na gode wa Allah da ka kama ni tun kafn in fara cin moriyar wannan kazamar harka.

“Na kuma shirya fuskantar hukuncin da za a yi min domin ya zama darasi ka masu son shiga wannan sa’ana,” in ji shi.

Advertisement

A wani labarin kuma Shugaban kamfanin BUA Abdul Samad ya ki karbar mukamin da APC ta ba shi

Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.

Advertisement

Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.

A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.

Advertisement

Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending