News
Hakkin tabbatar da zaman lafiya ya rataya a kan mu ne duka – Tinubu ga Gwamnoni
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Shugaban Kasa Bola Tinubu ya ce gwamnatin tarayya, jihohi da kananan hukumomi gaba daya ke da alhakin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a fadin kasar.
Da yake jawabi yayin wata ganawa da kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF) a gidansa da ke Legas ranar Talata, shugaban ya sake yin Allah wadai da kashe-kashen da aka yi a jihar Filato.
Gobara Ta Kone Shaguna 22 Tare Kadarori Na Miliyoyin Kudi A Kasuwar Gwarzo Dake Jihar Kano
Da yake jawabi ga gwamnonin, shugaban ya bayar da wani kakkausan umarni ga jami’an tsaro da su dakatar da kashe-kashen da ake yi a jihar Filato tare da kara zage damtse wajen zakulo wadanda suka haddasa munanan abubuwan da suka faru a kananan hukumomin Bokkos da Barkin-Ladi.
“Najeriya na bukatar zaman lafiya da kwanciyar hankali domin ci gaba, Najeriya ta mu ce kuma dole ne mu kula da ita. Kamar yanda Jaridar premium Times ta ruwaito
Bayan haka sai Tinubu ya jinjina wa gwamnan Ribas Simi Fubara, kan yadda ya amince da a zauna lafiya a
Jihar.
-
News3 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion6 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News2 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
