News
Gwamnatin Kano ta kaddamar da aikin gadojin sama na Dan Agundi da ta Tal’udu
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya ƙaddamar da aza harsashin aikin gadojin sama da za’ayi su a shatale-talen Tal’udu da Ɗan Agundi a yau juma’a da za’a kashe akalla Naira Biliyan 27.
Da yake karin bayani gwamnan jihar ta Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya kuma ce, aikin za’ayi shi ne domin samarwa al’umma sauki a fannin zirga-zirga, bisa yadda ake samun yawaitar cinkoso a guraren. dana ababan hawa
“Wannan aikin za’ayi shi ne haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin jiha da ƙananan hukumomin jihar mu domin aikin al’umma, “in ji Abba Gida-gida”.
A yayin ƙaddamar da aza harsashin aikin gadojin biyu dai gwamnan ya samu rakiyar mataimakin sa corm Aminu Abdulsalam Gwarzo, da tsohon mataimakin gwamnan jihar ta Kano Farfesa Hafiz Abubakar da sauran Kwamishinoni, da kuma sauran mutane. Kamar Yadda jaridar bustan daily ta rawaito
