Connect with us

News

Tirela Ta Kashe Mutum 6 Wasu 15 Sun Ji Rauni A Jihar Gombe

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

 

Mutane 6 sun mutu wasu 15 suka ji raunuka a wani hatsarin da wata tirela ta yi a hanyar Abacha Raod da ke unguwar Jekadafari a garin Gombe.

Kwamandan Hukumar Kiyaye Haddura ta Ƙasa a jihar Gombe, Felix Theman ne ya tabbatar da hakan a yammacin ranar Juma’a.

Cikakken Dalilin Shirin Ficewar ‘Shoprite’ Daga Jihar Kano

Ya ce tirelar tana dauke ne da shanu 27 da wasu yara a saman bodin ta.

Ya ce hanyar ta yi kadan wa manyan motoci su bi, amma masu tireloli suna kaunar bin ta, duk da cewa tana da kwane-kwane.

Advertisement

Aminiya ta ruwaito cewa Ya ce irin Yyran da suke hawan saman bodin motar sune suke yin ihu suna zuga direbobin su kuma suke kara gudu a cikin gari saboda burgewa da hakan ya kai su ga hatsari.

Daga nan sai ya ce za sun yi zama da masu ruwa da tsaki a harkar tukin manyan motoci dan jan kunnen direbobin tirelar da mafi yawan lokaci suke bai wa yaran motarsu suke ganganci a cikin gari domin kiyaye yawan aukuwar hatsari.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending