Connect with us

News

Yan Sanda Sun Kama Barayin Gadajen Daliban ‘Unity School’ a Jihar Jigawa

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Rundunar Yan Sanda a jihar Jigawa ta ce ta kama wasu mutane biyu bisa zarginsu da satar Gadaje da Katifun Daliban makarantar sikandiren Malam Madori (Government Unity Senior Secondary School GUSSS).

Mai Magana da yawun rundunar DSP Lawan Shiisu Adam ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya aikowa GLOBAL TRACKER.

2024: Sarkin Kudan Ya Taya Sarkin Zazzau Murnar Sabuwar Shekara 

Sanarwa ta ce “a ranar 27/12/2023 ne da misalin karfe ‘1500hrs’ wasu da ba’a san ko suwaye ba suka shiga makarantar, suka sace gadaje 19 na daliban na karfe da kuma Katifu guda hudu (4).’

Rundunar ta ce bayan samun rahoton ne ta bazama jami’anta suka kuma kama wani Muhammad Nadabo Mai shekaru 40 da Auwalu Muhammad Mai shekaru 34 dukkaninsu yan asalin Karamar Hukumar ta Malam Madori a jihar ta Jigawa.

Advertisement

 

“Da ake tuhumar wadanda ake zargi sun amsa lefin da ake zargin su da aikatawa” inji Sanarwar.

 

A wani cigaban labarin kuma, rundunar Yan Sandan jihar ta Jigawa ta kama wasu mutane biyu Abubakar Habibu Mai shekaru 12 Dan unguwar kofar Arewa a Karamar Hukumar Babura da wani Abdullahi Mujitafa mai shekaru 19 dan kofar Gabas a Karamar Hukumar ta Babura bisa zargin su da satar Gero wanda darajar sa ta kai naira dubu goma sha shida da dari biyar (16,500.00) da wasu kudi da yawan su ya kai naira dubu Arba’in da hudu (44.000.00).

DSP Shiisu ya ce wanda aka zargin an kama su ne bayan wani ya kai korafin anyi Masa sata na wadancan kayayyaki.

A lokacin da ake tuhumar su, sun amsa lefin su tare da bayyana sunan wata Habiba Haladu a matsayin wacce ta ke siyan dukkan kayan da suka Kai mata.

Advertisement

Sanarwar ta Kara da cewa dukkan wadanda ake zargi zaa mikasu Kotun da zarar ta Kammala bincike.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending