Uncategorized
Mustapha ya taya Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf murnar samun nasara a kotun ƙoli
DAGA AMINA SALISU BABA
Mataimakin shugaban kungiyar Youth Leader NNPP Kano dake karamar Hukumar Kano Municipal Mustapha Sagiru ya taya Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf murnar samun nasara a kotun ƙoli.
Hakan na kunshe ne ta cikin wata Sanarwa da ya turawa da Jaridar Inda Ranka a yau
Kotu ta yanke hukuncin mayar wa Najeriya fam miliyan 6.9 da aka sace
Sanarwar ta kara da cewa Hakika wannan nasara ba nasara ce ta jihar kano kadai ba, nasara ce ta Nigeria da Africa baki daya, haka kuma wannan nasara ta tabbatar da cewa damokradiyya ta zauna da gindinta a Nigeria.
Haka kuma ina godiya ga mai girma jagora Engr. Rabiu Musa Kwankwaso da yadda yayi uwa yai makarbiya a wannan shari’a
Ha kuma ina yabawa ‘yan majalisummu da suka ta bada tallafin Shanu, Rakuma, Raguna, Tumakai da kudade sauransu, domin yin addu’a ba dare ba rana.
Musamman ma dan majalisummu na kano Municipal a majalisar tarayya Engr. Sagir Koki bisa hidima da yayi na raba Raguna a dukkan mazabun karamar hukumar 13.
Haka kuma ina mai mika godiya ga ‘yan uwana shuwagabannin jam’iyyar NNPP na karamar hukumar Birni bisa yadda suka dage da addu’a badare ba rana har Allah ya tabbatar da wannan nasara,
Daga karshe bazan gushe ba sai na kara yiwa alummar jihar kano godiya bisa yadda suka dage da addu’a har wannan nasara ta tabbata.
Ina godiya ga yan uwa da abokan arziki da suka ringa Kirana a waya domin tayani murna da wannan nasara Allah ya saka da Alheri amen. Na gode naku Mustapha Sagiru Asst. Youth Leader NNPP Kano Municipal.