Connect with us

News

ECOWAS ta janye takunkumin da ta saka wa Nijar tsawan lokuta a baya

Published

on

Tinubu ecowas

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

Ƙungiyar ECOWAS ta janye takunkuman kasuwanci da ta saka kan Jamhuriyar Nijar. Haka kuma ƙungiyar ta sanar da janye takunkumin da ta saka wa kasar Guinea.
Kungiyar ta sanar da hakan ne a lokacin da take gudanar da wani taro a Abuja
TRT AFRICA HAUSA ta rawaito Ƙungiyar ECOWAS ta sanar da cewa za ta cire takunkumin da ta saka a kan Nijar wanda ya haɗa da batun rufe iyaka da kuma kasuwanci.

Ta bayyana haka ne a ranar Asabar a yayin taron da ta gudanar. Haka kuma ƙungiyar ta sanar da janye takunkumin da ta saka wa kasar Guinea.

Advertisement

Tun a farkon watan nan ne Mali da Burkina Faso da Nijar suka sanar da ƙungiyar kan niyyarsu ta barin ƙungiyar, wanda wannan sabon lamari ne tun bayan kafa ƙungiyar a 1975.

Sai dai tun a jawabinsa na farkom Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa: zasu dauki matakai daban daban

Advertisement

“Dole ne mu sake nazari kan hanyar da muka ɗauka ta neman tabbatar da mulkin dimokuraɗiyya a ƙasashe mambobinsu,” in ji Tinubu.

“Saboda haka ina kira a gare su da su sake nazari dangane da matakinsu na ficewa daga gidansu haka kuma kada su ɗauki ƙungiyarmu a matsayin abokiyar gaba,” kamar yadda ya ƙara da cewa.

Advertisement

An shafe lokaci mai tsawo ana dambarwa tsakanin ECOWAS da Nijar da Burkina Faso da Mali, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce. Sosai a mabanbantan sauran kasashe

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending