Connect with us

News

Bayan dage takunkumin da ecowas tayi Jamhuriyar Congo na,son Karfafa Zumuntar Hadin Gwiwa da china

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

Aleksandar Vučić: Yarjejeniyar Ciniki Cikin ‘Yanci A Tsakanin Sin Da Serbia Ta Bude Sabuwar Kofa Ga Bunkasuwar Serbia

Advertisement

Ministan harkokin wajen kasar jamhuriyar Congo Jean-Claude Gakosso ya bayyana a jiya cewa, kasarsa tana son yin hadin gwiwa da kasar Sin wajen karfafa dadadden zumunci da zurfafa hadin gwiwar moriyar juna da raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu yadda ya kamata.

 

Advertisement

An gudanar da liyafar murnar cika shekaru 60 da kulla dangantakar diplomasiyya tsakanin Sin da jamhuriyar Congo a wannan rana a fadar shugaban jamhuriyar Congo dake birnin Brazzaville, in,da minista Gakosso ya bayyana cewa, dangantakar Congo da Sin ta samu ci gaba sosai cikin shekaru 60 da suka gabata. Bangaren jamhuriyar Congo yana martaba ka’idar Sin daya tak a duniya, jamhuriyar Congo da Sin sun amince da juna da kuma yin hadin gwiwa a dukkan fannoni don amfanawa jama’ar kasashen biyu baki daya.

 

Advertisement

A nasa bangare, jakadan Sin dake jamhuriyar Congo Li Yan ya yi jawabin cewa, a cikin shekaru 60 da kulla dangantakar diplomasiyya a tsakanin Sin da jamhuriyar Congo, kasashen biyu sun nuna goyon baya da hadin gwiwa da juna, sun kasance abin misali na hadin gwiwa da sada zumunta a tsakanin Sin da Afirka. A matsayin wani sabon mafari na tarihi, kamata ya yi dukkan bangarorin biyu su aiwatar da muhimman shawarwarin da shugabannin kasashen biyu suka cimma bisa la’akari da ci gaba da kasancewa masu tabbatar da gaskiya da adalci, masu amana iri daya, abokan hadin gwiwar samun nasara, da yin mu’amala da koyi da juna, da karfafa hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare, da kafa ginshikin cikakken hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare, da ba da babbar gudummawa ga manyan al’ummomin Sin da Afirka masu kyakkyawar makoma, da kuma al’umma mai kyakkyawar makomar bai daya ga daukacin bil-Adama (Zainab Zhang)

 

Advertisement

 

SOURCE LEADERSHIP

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending