News
Gwamnatin Jihar Kano Ta Yi Alkawarin Hadin Gwiwa Da Kungiyar Mawallafa Jaridun Yanar Gizo Ta The Association of Online Media Guild
Gwamnatin Jihar Kano Ta Yi Alkawarin Hadin Gwiwa Da Kungiyar Mawallafa Jaridun Yanar Gizo Ta The Association of Online Media Guild
Kungiyar mawallafa jaridun yanar gizo ta The Association of Online Media Guild ta shirya taron karawa juna sani na kwana daya, wanda ya samu halartar ‘yan jaridu daga kungiyoyin yada labarai daban-daban a fadin jihar Kano.
A yayin bude taron, kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Baba Halilu Dantiye, ya yi jawabi ga mahalarta taron.
Da Ɗumi-Ɗumi-Ƴan Bindiga Sun Dira Wata Makaranta,Sun Yi Awon Gaba Da Ɗalibai A Kaduna
Ida ya taya Kungiyar mawallafa jaridar yanar gizo ta The Association of Online Media Guild, kuma muna ba ku tabbacin goyon bayanmu tare da idan akwai wuraren da za mu iya ba da tallafi, za mu yi hakan,” in ji Kwamishina Dantiye.
Ya jaddada mahimmancin yaki da labaran karya da ke da alaka da kafafen yada labarai na yanar gizo tare da bayyana banbance-banbance tsakanin kwararrun ‘yan jaridu da sauran su.
Dantiye ya bukaci a rika bin ka’idojin aikin jarida tare da karfafa gwiwar ‘yan jarida da su yi amfani da fasaharsu wajan samar da sahihan bayanai.
Sunusi Bature Dawakin Tofa babban sakataren Yada labaran Gwamnan Jihar Abba Kabir Yusuf Sunusi Bature , ya jaddada kyakkyawar alakar da ke tsakanin gwamnati da kafafen yada labarai. Ya yabawa kungiyar bisa samar da wani dandali na bunkasa aikin jarida a Jihar Kano
“Muna daukar kafafen yada labarai na yanar gizo da muhimmanci a gidan gwamnatin Kano. Za mu sake duba batun kafafen yada labarai na yanar gizo tare da Kungiyoyin Kafafan Yada Labarai ,” in ji Dawakin Tofa.
Shugaban kungiyar na rikon kwarya Abdullateef Abubakar Jos, ya bayyana kungiyar ‘yan jarida ta yanar gizo a matsayin kungiyar ‘yan jarida da ke aiki ta yanar gizo tare da mambobinta a fadin Najeriya, mai hedikwata a Kano. Ya jaddada kudurin inganta aikin jarida na da’a da kuma isar da sahihan labarai.
A karshen taron, mahalarta taron sun karbi takaddun shaida, wanda ke nuna nasarar kammala shirin na kwana daya.
-
News3 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion6 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News2 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
