Connect with us

News

Yadda mahara suka sungumi almajirai a Sokoto, kwana biyu bayan jidar ɗalibai 287 a Kaduna

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Rahotanni sun tabbatar da cewa aƙalla almajirai 15 aka arce da su zuwa cikin daji, a wani farmakin da aka kai musu lokacin da suke tsakiyar barci a ƙauyen Gidan Bakuso, cikin Ƙaramar Hukumar Gada cikin Jihar Sokoto, a ranar Asabar da jijjifin safiya.

Sace almajiran ya zo kwanaki biyu kacal bayan sace ɗalibai 287 a ƙauyen Kiriga cikin Jihar Kaduna.

Yanzu – Yanzu Gobara ta tashi a Gidan Wutar Lantarki dake Dan Agundi

Shi kuma ƙauyen Gidan Bakuso ya na gabacin jihar Sokoto ne, kuma ya haɗa kan iyaka da Jamhuriyar Nijar.

An ce maharan sun fara da afkawa cikin wani gida, inda suka ɗauki wata mace, daga nan suka yada zango a makarantar da almajiran suke.

“Maharan sun yi awon gaba da mace, su na cikin tafiya ne sai suka ci karo da makarantar tsangayar da almajiran ke karatu, kuma a ciki su ke kwana.

Advertisement

“Almajiran su na tsakiyar barci a waje, sai dai suka ji ƙarar baburan da ‘yan bindiga su ka shiga ƙauyen da su. Kuma suka ji wata mace na ta kuka. Daga nan sai almajirai kowa ya tashi ya fece a guje cikin gidaje daban-daban.”

Haka dai Liman Abubakar, mai makarantar tsangayar ya bayyana wa Sashen Hausa na VOA.

“Zuwa yanzu dai mun ƙirga mun ga babu almajirai 25, waɗanda har yanzu muke neman su ba mu gani ba.”

Wani ɗan siyasar ƙauyen ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa mazauna garuruwan Gada, Goronyo, Isa da Sabon Birni duk ƙarƙashin ikon ‘yan bindiga su ke.

“To mu dai ‘yan adawa ne. Idan muka faɗi wata magana, cewa za su yi muna tsarma siyasa a batun matsalar.

“Amma dai maganar gaskiya, kwashe almajirai da aka yi abu ne da za a iya kauce masa.

Advertisement

“Saboda ‘yan bindiga sun shiga, sun yi harbi sama, sun kwashi almajirai, amma babu wani hoɓɓasa daga ɓangaren jami’an tsaro.

Wani Ɗan majalisa daga Gada mai suna Kabiru Dauda, ya ce matsalar tsaro a yankin sai ƙara taɓarɓarewa ta ke yi.

Kakakin ‘Yan Sandan Sokoto, Ahmad Rufai ya tabbatar wa wakilin mu cewa yara 15 aka arce da su sai kuma mace guda ɗaya.

Ya ce ‘yan sanda sun bazama neman maharan domin su ceto almajiran.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending