Connect with us

News

Yadda jami’ar Hukumar Tara Haraji ta karkatar da kuɗaɗen haraji cikin makarantar kuɗi da ta gina

Published

on

Spread the love

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI TUKUNTAWA 

A ci gaba da wata shari’a, wadda EFCC ta maka wadda ake zargi da karkatar da Naira biliyan 2, mai gabatar da shaida a gaban kotu, ya shaida wa Mai Shari’a a Babbar Kotun Tarayya ta Abuja yadda Shugabar Sashen Masu Ruwa da Tsaki na Hukumar Tara Kuɗaɗen Haraji ta Ƙasa (FIRS), mai suna Emmanuella Ita, ta karkatar da maƙudan kuɗaɗen haraji zuwa amfanin kan ta da kan ta.

Premium Times ta ruwaito cewa a ranar Litinin, mai gabatar da shaidu ta ce Emmanuela ta yi amfani da kuɗaɗen wajen gina makarantar kuɗi, mai suna Surestart School Ltd.

Kotu Ta Umurci Binance Da Ya Bai Wa EFCC Bayanan Duka Masu Hada-Hadar Kudade Ta Shafinsa A Najeriya

Emmanuela Ita, ta mallaki makarantar a lokacin da kuma ta na shugabancin sashe sukutum a Hukumar Tara Haraji ta Ƙasa, kamar yadda wata sanarwar manema labarai da Hukumar EFCC ta raba ta nuna, a ranar Litinin.

Advertisement

Da ta ke bayar da shaida, matsayin mai bayar da shaida na shida a ranar Litinin, Ijeoma Maltida, wadda jami’ar bincike ce ta EFCC, ta shaida wa kotu cewa Ita ta karkatar da kuɗaɗen ayyukan Hukumar EFCC.

Lauyoyin wadda ake ƙara sun yi wa mai gabatar da shaida tambayoyi. Babban lauyan ta Paul Erokoro, SAN, ya ce an gano kuɗaɗen a asusun ajiyar ta ɗauke da bayanin cewa kuɗin ayyukan Hukumar FIRS ne.

Ta shaida wa Mai Shari’a Folashade Ogunbanjo-Giwa cewa masu bincike sun gano waɗannan kuɗaɗe ne dai aka tura kai-tsaye a cikin asusun bankin Surestart School Ltd, makarantar wadda ake zargi da karkatar da kuɗaɗen.

“Lokacin da ta zo ofis ɗin mu, mun ɗauki bayanan ta, kuma mun bi ta da lalama, mun girmama ta sosai.

Advertisement

“Lokacin da ta ke wurin mu domin tantance tsaki da tsakuwa, ta fara fito da kwafen takardun bayanai, kuma ta amince za ta biya wasu kuɗaɗen da aka kasa gano yadda aka yi da su.

“Ta shaida a cikin bayanin da yi a hannun mu cewa za ta biya kuɗaɗen. To ban san inda ta samo kuɗaɗen ba, domin har ta dawo da Naira miliyan 17. Amma cewa ta yi Naira miliyan 5 kaɗai ta ci a baki ɗayan kuɗaɗen da aka karkatar ɗin.”

Haka bayanin EFCC ya ƙunsa.

Mai gabatar da shaida na EFCC ya ce sun gano a cikin harƙallar har da wani mai suna Daniel, wanda aka ce ya mutu. “Mun nemi a ba mu katin satifiket na shaidar mutuwar sa, kuma an ba mu. Mun je banki mun sa an buɗe mana asusun ajiyar sa, mun ga lallai shi ma ya ci kuɗin kafin mutuwar sa.”

Advertisement

Yanzu dai an ɗage ci gaba da shari’ar zuwa ranakun 20 da 21 ga Maris.

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *