News
An Gurfanar Da Mutum Biyu A Kotu Bisa Zargin Satar Waya Ta Naira Miliyan 1.9
Kotun Majistare da ke Wuse, Abuja, ta gurfanar da mutum biyu, Shittu Olatunji da Fatima Audu, bisa zargin satar wayoyi guda biyu da darajarsu ta kai Naira miliyan 1.9.
Lauyan mai gabatar da ƙara, Simpa Ibrahim, ya bayyana a gaban kotu cewa wanda ya kai ƙarar, Bashiru Badamosi, ya shigar da rahoton lamarin a ofishin ’yan sanda na Garki a ranar 29 ga watan Agusta.
A cewarsa, yayin da Badamosi ke tafiya a kan titin Lagos Crescent da ke Garki, waɗanda ake tuhumar suka karɓe masa wayoyi biyu – Samsung A15 da Samsung Z Fold 5 – waɗanda jimillar kudinsu ta kai Naira miliyan 1.9.
Ibrahim ya ƙara da cewa laifin ya sabawa sashe na 79 da 287 na Dokar Penal Code.
Sai dai, waɗanda ake tuhumar sun musanta aikata laifin da ake zarginsu da shi.
Lauyan kariya, Enagonimi Ekpede, ya roƙi kotu da ta ba su bel bisa tanadin sashen 165 na Dokar Gudanar da Shari’o’in Laifi (ACJA), inda ya nemi a yi hakan cikin sauƙin sharudda.
Mai shari’a Ekpeyong Inyang ta amince da bayar da belin su kan Naira miliyan 1 kowanne. Daga nan ta dage sauraron shari’ar zuwa ranar 12 gawatan Oktoba.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
