News
Hukumar Kwastam ta kama haramtattun kaya na miliyoyin naira a Kaduna
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI TUKUNTAWA
Hukumar Kwastam dake kula da shiyar Zone B a jihar Kaduna ta bayyana cewa ta kama haramtattun kaya 98 a cikin watanni biyu a jihar.
Premium Times ta ruwaito cewa Shugaban hukumar Dalha Chedi ya sanar da haka ranar Alhamis a garin Kaduna.
Ya ce daga ranar 17 ga Fabrairu zuwa Maris 28 hukumar ta kama haramtattun kaya da kudaden su ya haura miliyoyin naira.
“Daga cikin kayan da aka kama akwai Shinkafa, takalma man fetur, taliya, macaroni, couscous, kayan sawa, man gyada da motocin tokunbo.
Chedi ya yi kira ga ‘yan sumoga da su daina shigo da kayan da gwamnati ta hana shigowa da su, yana mai cewa hakan na kawo wa tattalin arzikin kasa cikas.
Ya yi kira ga masu motocin da su tabbatar sun hada takardun motocin su domin guje wa fada wa hannun hukuma.