Connect with us

Labarai

Hukumar EFCC ta ce ta kwato naira biliyan 30 a karkashin badakalar Betta Edu

Published

on

Advertisements
WhatsApp Image 2026 11 04 at 12.03.38 AM

 

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Ya zuwa yanzu dai, Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa zagon kasa (EFCC) ta kwato wa Gwamnatin Tarayya Naira Biliyan 30, yayin da ta kuma sanya asusun ajiyar banki 50 a binciken da ake yi wa tsohuwar ministar harkokin jin kai da yaki da fatara, Betta Edu da wata ma’aikaciyar Ma’aikatar, Halima Shehu.

Kimanin watanni uku da suka gabata ne shugaba Bola Tinubu ya dakatar da Betta Edu da Halima Shehu saboda zargin karkatar da makudan kudade.

Bankin kasa CBN ya sake karya farashin Dalar Amurka domin farfaɗo da darajar Naira.

Nan take kuma, Shugaban ya dakatar da shirin na Tallafi da rage talauci (NSIP), sannan ya bukaci hukumar EFCC da ta binciki jami’an da ke da hannu acikin badakalar.

Leadership ta ruwaito cewa Bayan watanni uku, shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyede, wanda ya bayyana haka, ya ce, hukumar na samun nasarorI a binciken.

Advertisement

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending