Connect with us

News

Tun ba a kai ko ina ba, Abba da maƙarraban sa sun kiɗime, sai kame-kame su ke yi da neman raba kan jama’a a Kano – Ganduje

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Shugaban jam’iyyar APC ta kasa, Abdullahi Ganduje, ya gargaɗi gwamna Abba Yusuf na jihar Kano da ya daina amfani da dabarun raba kan jama’a wajen fakewa da gazawar sa ga al’ummar jihar.

Kakakin Ganduje Edwin Olofu ya bayyana a wata sanarwa da ga Ganduje cewa ɓaɓatu kawai gwamna Yusuf yake yi saboda ya gaza nuna wani abu da ya yi a Kano tun bayan ɗarewar sa gwamnan jihar, duk da dimbin kuɗin da ake dankara wa Kano daga Abuja.

Za mu gabatar da kudurin kin amincewa da ƙarin kuɗin Wutar lantarki – Sanata Ndume

Gwamna Ganduje na mayar da martani ne kan matakin da gwamnatin jihar Kano ta dauka na gurfanar da shi a gaban kotu bisa zarginsa da karbar cin hancin dala 413,000, da kuma Naira biliyan 1.38.

” Maimakon gwamnatin Kano ta maida hankali wajen tabbatar da samun wadata da walwale a tsakanin mutanen jihar sun karkata ne wajen dole-dole su fallasa zargin da ba su da iko aka sa.

” Saboda rashin sani da karancin Ilimi da ya dabaibaye Abba da maƙarrabansa, sun manta cewa akwai umarnin kotun tarayya da ta ce wannan batu na cin hanci ba ya karkashin jiha, shari’a ce ta gwamnatin tarayya.

Advertisement

” Amma za su iya komawa su gyara kurakuransa ta hanyar bin turakun da muka daddasa su yi koyi da yadda muka yi ayyukan mu a baya.

A karshe ya ce zai fi dacewa innda gaske ne gwamnati ke yi, ta faro bincikenta tun daga 1999 ne, idan da gaske babu lauje cikin naɗi.

 

 

Premium Times

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending