News
‘Yan Majalisar Tarayya su 60 sun yi barazanar ficewar daga PDP, tare da neman a cire Shugaban Riƙo na PDP na Ƙasa
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
‘Yan Majalisar Tarayya su 60 sun yi barazanar ficewar daga PDP, tare da neman a cire Shugaban Riƙo na PDP na Ƙasa, Bello Damagum.
‘Yan Majalisar sun yi zargin cewa ana ƙulle-ƙullen ƙaƙaba wa PDP wasu jami’an APC a matsayin mambobin riƙon ƙwarya, domin tsara wani ɓoyayyen shirin su.
Hukumar EFCC ta ce ta kwato naira biliyan 30 a karkashin badakalar Betta Edu
Premium Times ta ruwaito cewa sun yi wannan barazanar ce sakamakon rikicin da ya dabaibaye PDP a Jihar Ribas da wasu jihohi 10.
Ɗan Majalisar Tarayya Ikenga Ugochinyere daga Jihar Imo ne shi da wasu mambobi 5 suka gabatar da wannan gargaɗin, a wurin wani taron manema labarai, a Majalisar Tarayya, a Abuja, ranar Litinin.
Sun kuma nemi a cire Shugaban Riƙo na Jam’iyyar PDP, Umar Damagum, kafin taron Majalisar Zartaswar PDP mai zuwa.
Su shida ɗin sun ce su na magana ne a madadin ‘yan Majalisa 60 na PDP, inda PDP ɗin ke da mambobi 100 da ɗoriya.
“Ba zai yiwu a ce APC ce ke gudanar da ikon jam’iyyar PDP ba. Ba zai yiwu ‘yan APC su zama shugabannin PDP a Jihar Ribas da wasu jihohi 10 ba.
“Ya kamata duniya ta sani cewa ana ƙulle-ƙullen sai an ƙaƙaba APC a shugabannin jam’iyyar PDP na riƙo ba. Wani babban shiri ne suke ƙullawa.”
-
News14 hours ago
Jam’iyyar Labour Party Ta Yi Alkawarin Kafa Hukumar Kula Da Hayar Gidaje A Kano
-
News3 days ago
Shettima @60: Haƙurinsa, Biyayyarsa Sun Taimaka Wajen Ciyar Da Manufofin Shugaba Tinubu Gaba — Kwankwaso
-
News6 days ago
KANO:’Yan Mata Uku ’Yan Gida Ɗaya Sun Mutu A Kifewar kwale-kwale A Tiga
