Entertainment
A Ƙarshe Dai Jaruma Mansura Isa Ta Sake Ɗaura Aure
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI
A wani faifan bidiyo da tsohuwar jaruma Samera Ahmad ta wallafa an hangi jama’a zagaye da jaruma Mansura Isa inda aka ji Samera tana cewa an ”ɗaura an ɗaura a kunna mana wutan.”
Sauran mutanen da ke kewaye ma ba a bar su a baya ba wajen tofa na su albarkacin bakin inda ɗaya daga cikin su ta fashe da guɗa.
Hukumar EFCC Ta Sanya Tukwici Ga Masu Fallasa Waɗanda Ke Wulaƙanta Kuɗin Naira
Haka kuma an ga jaruma Mansura Isa an mika mata kuɗaɗen a cikin leda inda Samera ke cewa ga su sun iso,” ta nuna a hannun mu”,Wato sadaki Naira N1,000,000