Connect with us

News

Idan gwamnoni suka rage cin hanci za su iya biyan fiye da N60,000 —Ƙungiyar ƙwadago

Published

on

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA 

Ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya NLC ta ce gwamnonin jihohin ƙasar za su iya biyan foye da naira 60,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi, idan suka rage cin hanci da rashawa da kuɗin da suka kashewa wajen gudanar da mulki a jihohinsu.

Advertisement

Aranar Juma’a ne dai ƙungiyar gwmanonin ta fitar da wata sanarwar da a ciki take cewa gwamnonin jihohin ƙasar 36 ba za su iya biyan naira 60,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi ga ma’aikata ba.

Wani Gungun ‘Yan Ta’adda Sun Fille Kan Matasa 10 A Jihar Neja

To sai dai a cikin martanin da ta mayar ƙungiyar ta NLC, ta yi Allah wadai da sanarwar gwamnonin.

Advertisement

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun NLC, Benson Upah,ya fitar ya ce idan gwamnaonin suka mayar da hankali babu abin da zai hana su biyan mafi ƙarancin albashin.

”Koda nawa ne mafi ƙarancin albashi ba ma naira 60,000 ba, in suka rage kuɗin da suke kashewa wajen gudanar da gwamnati, sannan suka rage cin hanci da rashawa to za su iya biya domin tabbatar da walwalar ma’aikata”, in ji sanarwar.

Advertisement

Bbc hausa ta ruwaito cewa A ranar Juma’a ne bayan wata ganawa da wakilan gwamnati ƙungiyar ƙwadagon ta buƙaci gwamnatin tarayya ta biya naira 250,000 a matsayin maf ƙarancin albashi

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending