Connect with us

News

Aikin Gyare-Gyaren Titin Eastern Bypass Ya Yi Sanadiyar Mutuwar Mutum 6 A Kano 

Published

on

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA 

Aikin gyare-gyaren titin Eastern Bypass a cikin birnin Kano ya yi sanadiyar mutuwar mutum shida cikin makonni uku zuwa hudu.

Advertisement

Jaridar Nigerian Tracker ta ruwaito cewa cewa wani sashe na hanyar da ke kusa da gidan mai na Chula ana yin gyara duk shekara. Wannan ya sa aka buƙaci rufe hanya ɗaya don ba da damar gyarawa.

Idan gwamnoni suka rage cin hanci za su iya biyan fiye da N60,000 —Ƙungiyar ƙwadago

Sakamakon gyare-gyaren da wata hukumar gwamnatin tarayya da ke da alhakin gyara lalacewar hanyar ta yi, jama’ar da ke zaune a kewayen na cikin fargaba a koda yaushe.

Advertisement

Yanzu   mutane shida ne suka mutu a lokacin da suke yunkurin tsallaka hanyar.

A safiyar yau Asabar, wani matashi mai suna Amir Suleiman, ya mutu a lokacin da wata babbar mota kirar tipper da ke gudu a kan titin daya daga cikin hanyoyin da aka rufe ta murkushe shi.

Advertisement

Mahaifinsa, Malam Suleiman, ya shaida wa NIGERIAN  TRACKER cewa ya samu wannan mummunan labari ne a lokacin da yake halartar sallar jana’iza da misalin karfe 7 na safe, ya garzaya gida domin shirya jana’izar dansa.

Mazauna Yandodo, Muhibba, Unguwar Kwari, da Hotoro ta Arewa suna kira ga hukumomi da su magance matsalar cikin gaggawa.

Advertisement

Sun ba da shawarar ko dai a sa dan kwangilar ya yi aiki da daddare don ba da damar yin amfani da hanyoyin biyu da rana ko kuma a hanzarta kammala aikin.

Bugu da kari, sun bukaci jami’an tsaro da su sanya ido sosai kan yadda manyan motoci ke amfani da hanyar don hana afkuwar hadura.

Advertisement

A makon da ya gabata, an murkushe wani yaro har lahira a daya titin. Sai da aka fitar da gawarsa da felu domin binne shi. Rahotanni sun nuna cewa ba a nuna wa mahaifin yaron gawar ba saboda munin hatsarin.

Al’umma na ci gaba da yin kira da a dauki matakin gaggawa don hana sake samun asarar rayuka.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending