Connect with us

News

Da Alama Talauci Da Tsadar Rayuwa Za Su Kashe Armashin Babbar Sallah A Bana

Published

on

DAGA YASIR KABIRU MUHAMMAD 

A ranar Lahadi mai zuwa ce za a gudanar da Babbar Sallar bana, inda masu hali daga cikin Musulmi suke yanka dabbbin Layya da sauran hidindimu.

Advertisement

Jaridar INDA RANKA ta zagaya domin ganin yadda farashin dabbobin Layya da sauran kayan masarufi da kuma yanayin tafiye-tafiye suke.

Aikin Gyare-Gyaren Titin Eastern Bypass Ya Yi Sanadiyar Mutuwar Mutum 6 A Kano 

Wakilanmu sun gano cewa farashin dabbobi ya ninka na bara a fadin Najeriya, wanda bai rasa nasaba da tashin farashin man fetur da karyewar darajar Naira ba.

Advertisement

A Jihar kano wakilin Jaridar INDA RANKA da ya kewaya kasuwannin dabbobi a Kano ya tarar a Kasuwar Yan Awaki farashin rago ya fara ne daga Naira 150,000 zuwa 300,000. 500,000 1,000,000

A wasu kasuwanni kuma, farashin rago ya kama daga Naira 60,000 zuwa Naira 320,000.

Advertisement

A Jihar Kano Sallar ta zo da sauye-sauye da dama kama daga kan yadda ake gudanar da cinikin dabbobi da kuma yadda ake hada-hadar kayan Sallah da kayayyakin abinci.

A zantawarmu da Daya daga cikin masu sayar da dabbobin sun ce yanayin cinikin dabbobin ya ragu sosai idan aka kwatanta da bara.

Advertisement

“A bana abubuwa sun sauya matuka. Hakan ya faru ne sakamkon faduwar daarajar Naira da kuma janye tallafin man fetur da aka yi.

“Mutane babu kudi a hannunsu a bana, shi ya sa ba a zuwa saya sosai. Ga tsada ga kuma rashin kudi a hannun mutane,” wani mai sayar da dabbobi, ya bayyana wa wakilinmu.

Advertisement

Sai dai a lokacin ziyarar da ta kai wasu kasuwanni a jihar Kano buhun masara mai nauyin kilogiram 100 da ake siyar da shi kan Naira 60,000 a makon jiya yanzu a kai N70,000 zuwa sama; Buhun shinkafar gida 100kg yanzu ya koma N129,000 sabanin N106,000 da aka sayar makwannin da suka gabata yanzu N90,000 zuwa N95,000, yayin da buhun barkono ya kai N109,000.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending