Connect with us

News

Saukar da Farashin Kayayyaki Ƴan Najeriya ke buƙata, ba kara mafi karancin albashi ba

Published

on

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA 

Wani Jigo a Jam’iyyar PDP a Jihar Delta Sunny Onuesoke ya ce, ƙarin mafi karancin albashi ba shine maganin matsalar tsadar rayuwa da ake fuskanta ba, illa saukar da farashin kayayyakin abinci da sauran kayan amfanin yau da kullum.

Advertisement

Ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da ya yi da wakilinmu a wani martanin da ya mayar dangane da yadda take kasancewa tsakanin Gwamnatin Tarayya da kungiyoyin kwadago a kasar nan.

Da Alama Talauci Da Tsadar Rayuwa Za Su Kashe Armashin Babbar Sallah A Bana

Onuesoke ya ce ƙarin albashin ba zai magance matsalar tattalin arzikin kasar ba face ma ya ƙara dagula al’amurra.

Advertisement

Ƴan Najeriya suna yaudarar kan su ne kawai, amma abinda ake bukata a yanzu shine rage farashin kayayyaki. Idan za a kara albashi zuwa Naira Miliyan ɗaya a yau, to haka ma farashin kayayyaki zai cigaba da ƙaruwa.

Da zarar an ƙara mafi karancin albashi to haka farashi zai ƙara karuwa, Saboda Talakawan da ba Ma’aikatan Gwamnati ba da ke samar da kayan abinci kamar Tattasai, Doya da sauransu za su ƙara farashi.

Advertisement

A cewar Cif Onuesoke ” Karin albashi ba zai iya magance hauhawar farashin kayayyaki ba, saboda yadda ake samun karin albashi akwai karin kudin da ke yawo a tsarin. Yayin da aka samu yawaitar yawon kuɗi a hannun Jama’a kuwa, to hakan zai ƙara haddasa hauhawar farashi, wannan ɗan ƙaramin lissafin tattalin arziki ne da ba kowa ke iya fahimta ba.

Ba Ma’aikatan Gwamnati ne kaɗai ke tafiyar da ƙasar ba, Ma’aikatan Gwamnati kaso 14 ne cikin 100 kacal. Ma’aikatu masu zaman kan su kuwa ba duka bane za su iya biyan wannan adadin a matsayin albashi a kowane wata”

Advertisement

Ya ce abin da ‘yan Najeriya ke bukata a halin yanzu shi ne rage hauhawar farashin kayayyaki ta yadda ko da ma’aikaci yana karbar Naira dubu 20 a matsayin mafi karancin albashi to ya iya biyan kudin hayar gidan sa, da kuma biyan sauran bukatun sa cikin kwanciyar hankali.

Ya kuma bukaci Gwamnatin Tarayya da ta kara kaimi wajen gina gidaje masu saukin kudi domin baiwa talaka tallafi da zai mora na tsawon rayuwarsu a matsayin hanyar rage hauhawar farashin kayayyaki.

Advertisement

Jama’a na bukatar ababen more rayuwa da za su rage wahalhalun da suke ciki, Abin da nake cewa shi ne Gwamnatin Tarayya da Gwamnonin Jihohi su kara kaimi ga ayyukan noma da gina gidaje masu dumbin yawa domin bada tallafi, da rage kuɗaɗen Asibiti.

Matsalarmu ita ce muna magani daban ciwo daban akan matsalolin ƴan Najeriya, idan ka tambayi shugabanninmu kadada nawa ne za su samar da adadin rogo kaza? ba su sani ba, Amma sun iya cika baki akan alƙalumman hasashe.

Advertisement

kowace karamar hukuma ya kamata ta samu kadada 80,000 na gonakin rogo, da Doya, da Masara, da Shinkafa da dai sauransu, sannan a gyara matatun mai, Me ya hana kasar gyara matatun Mai hudu da muke da su? har gobe Rashin gyara matatun Mai yasa muke shigo da shi daga waje, sannan kuma har gobe Najeriya ce kasa ta shida da tafi hako mai a duniya”

Karin mafi karancin albashin dai kari ne na Naira dubu biyu da Gwamnatin Tarayya tayi wanda tace zai zarce tayin farko na Naira dubu sittin.

Advertisement

Kungiyar kwadago kuwa ta rage dogon buri daga Naira dubu dari hudu da casa’in da hudu 494,000 zuwa Naira 250,000 duk wata.

Bangarorin biyu dai ba su kai ga cimma matsaya kan lamarin ba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending