Connect with us

News

Kungiyar kwadagon ta NLC/TUC ta ce ko N100,000 ta yi kadan a matsayin mafi karancin albashi.

Published

on

Spread the love

DAGA UMAR IBRAHIM HOTORO 

 

Kungiyar kwadagon Nijeriya ta ce ko N100,000 ta yi kadan a matsayin mafi karancin albashi.

Advertisement

Kungiyar ta nanata cewa ya kamata gwamnati ta amince da bukatar N250,00 kawai a wuce wurin.

A yau Litinin ake saka ran za a ƙarkare tattaunawa kan mafi ƙarancin albashi tsakanin Gwamnatin Nijeriya da Ƙungiyar Ƙwadago ta NLC/TUC bayan dawowar ƙungiyar daga halartar wani taro a ƙasar Geneva.

Ƙungiyar Ƙwadagon dai ta rage farashin abunda ta ke buƙata daga ₦494,000 zuwa ₦250,000 inda ita ma gwamnatin Nijeriya a nata bangaren ta yi alƙawarin ƙara ₦2,000 daga tayin ₦60,000 zuwa ₦62,000.

Advertisement

Yawan Sare Bishiyu Da Mutane Keyi Zai Iya Haifar Da Yawan Cututtuka Da Kuma Karancin Abinci —Masani A Bangaren Aikin Gona

Kawo dai yanzu kallo ya koma kan gwamnatin Nijeriya da Ƙungiyar Ƙwadago don ganin ko za su iya samun daidaiton da ya dace da bukatun juna, la’akari da ƙalubalen tattalin arzikin da ƙasa ke fuskanta.

Leadership ta ruwaito cewa A makon da ya gabata Kungiyar Kwadago ta shiga yajin aikin gama-gari a fadin kasar kafin daga bisani kungiyar ta janye bayan kiraye-kirayen komawa teburin sulhu da tsagin gwamnati don samun daidaito.

Advertisement
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *