News
DA DUMI DUMI: ‘Yan Jarida Sun Kauracewa Dukkanin Wasu Harkoki Na Gwamnatin Jihar Kano Ba Tare Da Wani Bata Lokaci Ba
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Kungiyar wakilan kafafen yada labarai ta kasa, ta ce ta kauracewa dukkanin wasu harkoki na gwamnatin Jihar Kano ba Tare da Wani bata Lokaci ba.
Matakin hakan na kunshe cikin Wata sanarwar da shugaban kungiyar Aminu Ahmed Getso ya sanyawa hannu a litinin din nan.
NPFL: Kungiyar Kwallon Kafa Ta Doma United Ta Yi Hatsarin Mota
Aminu Ahmad Getso ya bayyana cewa sun dauki wannan mataki ne saboda kyara, da cin Fuska da tsangwama da ya ce wakilan nasu na fuskanta daga gwamnati da wakilanta yayin gudanar da aiyukansu
Kazalika kungiyar ta koka kan yadda ta ce, gwamnatin na amfani da wadanda ba yan yaridu ba wajen daukar harkokin gwamnati, maimakon barin yar jaridu su yi aikinsa bisa kwarewa.
Saboda haka ne kungiyar ta ce daga yanzu ba zata sake halartar taron yan jaridu, ko wata ganawa da wakilan gwamnati ba, har sai an samu gyara kan ‘yanci da kuma kare lafiyar yan jaridu a fadin jihar.
Ana Samun Korafe Korafe akan Yadda Gwamnatin Jihar Kano take Watsi da ka’idar aikin Jarida Wajen baiwa Yan Siyasa Damar Wasu ayyuka Wanda Kuma hakan ya Saba da Dokar aikin Jarida
Ko a Hawan Karamar Sallah da ya gabata sai da aka samu wata Hatsaniya a Gidan Gwamnatin Jihar Kano Tsakanin Wani Jami’in Gwamnati da Kuma wasu Yan jaridu sakamakon Kokarin shiga Aikin Yan Jarida da akeyi.
https://www.facebook.com/share/p/yqVMSjfCtnLptGuw/?mibextid=oFDknk