Sports
NPFL: Kungiyar Kwallon Kafa Ta Doma United Ta Yi Hatsarin Mota

DAGA UMAR IBRAHIM HOTORO
Kungiyar kwallon kafa ta Doma United, ta yi hatsarin mota ranar Litinin kamar yanda Jaridar DAILY POST.
Rahotanni na nuni da cewa ba a samu asarar rai ba amma ‘yan wasa da dama ne suka jikkata a lamarin.
‘Yan wasan da suka samu raunuka na samun kulawa a asibiti.
Hadarin ya afku ne akan hanyar Makurdi-Lafia.
Doma United na kan hanyarsu ta dawowa daga Owerri bayan karawar da suka yi da Heartland ranar Lahadi.