Connect with us

Sports

Kylian Mbappe Zai Sa Riga Mai Lamba 9 A Sabuwar Kungiyarsa

Published

on

Spread the love

DAGA UMAR IBRAHIM HOTORO 

Sabon dan wasan Real Madrid, Kylian Mbappe, ya saka hannu kan kwantiragin komawa Real Madrid daga Paris St-Germain, idan yarjejeniyarsa ta kare ranar 30 ga watan Yuni.

Tun cikin watan Fabrairu dan wasan na tawagar Faransa ya amince baka da baka da cewar zai koma Sifaniya, sannan cikin watan Mayu aka sanar da zai bar PSG a karshen kakar nan.

Advertisement

Tashin Hankali: Wani Shirgegen Mesa Ya Hadiye Wata Mata Da Ranta.

Mbappe mai shekara 25 a duniya ya saka hannun kan kunshin yarjejeniyar da Real Madrid ta gabatar masa, wanda zai koma Sifaniya ranar 1 ga watan Yuli da za a bude kasuwar cinikayyar ‘yan kwallo a La Liga.

Tuni Real Madrid ta sanar da labarin kammala kulla kwantiragi da Mbappe na tsawon shekara biyar kuma a nan gaba ne kungiyar za ta gabatar da shi gaban magoya baya a Bernabeu kafin fara Euro 2024. Mbappe ya lashe kofin duniya a 2018, kuma shi ne kan gaba a yawan cin kwallaye a PSG mai 256 a raga, tun bayan da ya koma kungiyar aro daga kungiyar Monaco a shekarar 2017.

Leadership ta ruwaito cewa Ya amince da yarjejeniyar da za ta kare a Real zuwa karshen 2029, sannan kuma zai dinga karbar albashin fam miliyan £12.8m a kowacce kakar wasa da karin ladan £128m da za a biya cikin shekara biyar, kuma zai rike kudin tallace-tallacensa. Sannan zai samu damar buga wasa tare da dan wasa Luca Modric, yayin da dan kwallon Croatia zai kara sa hannu kan yarjejeniyar kakar wasa guda daya a Real Madrid.

Advertisement

Modric, mai shekara 38, ya shiga wasa daga baya ranar Asabar da Real Madrid ta lashe Zakarun Turai na 15 jimilla, bayan da ta doke Borussia Dortmund a Wembley.

Kwantiragin tsohon dan wasan Tottenham din zai kare a karshen watan nan a Real Madrid, amma ana sa ran za a tsawaita masa kaka daya kamar yadda shugaban gudanarwar kungiyar Florentino Perez ya bayyana.

Real Madrid ce ta lashe gasar La Liga na bana kuma na 36 jimilla da tazarar maki 10 tsakaninta da abokiyar hamayyarta wato Barcelona, wadda ta yi ta ukun teburin babbar gasar ta 2023 zuwa 2024.

Advertisement
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *