Connect with us

News

Yawan Sare Bishiyu Da Mutane Keyi Zai Iya Haifar Da Yawan Cututtuka Da Kuma Karancin Abinci —Masani A Bangaren Aikin Gona

Published

on

Spread the love

DAGA ABDUL RAHAMAN MUHAMMAD 

Masani a bangaren aikin gona kuma malami a Jami’ar kimiyya da fasaha ta Aliko DanGote Dake Wudil Dakta Munir Abdulmumin Yawale yace rashin dashen bishiyu da kuma yawan saresu da mutane keyi zai iya haifar da yawan cututtuka da kuma karancin abinci a Najeriya

Dakta Munir Yawale ya bayyana hakane yayin taron kaddamar da dashen bishiyu wanda ya gudana a Unguwar zawachiki da yammacin jiya wanda ƙungiyar Make Zawachiki Green karkashin jagorancin shugabancin Daliban Unguwar zawachiki.

Advertisement

Makarantar Koyar Da Sana,oi Ta Fauza Tailoring Center Tayi Bikin Yaye Dalibinta 39.

Yana Mai cewa indai za,a ke sare bishiyu to la shakka za,a tsunduma cikin dumamar yanayi, da zaizayewar kasa, da samun ambaliyar ruwa da kuma samun karancin ruwan sama, yayin da yawan dashenta kuma zai taimaka wajen samun ingantacciyar lafiya da kuma rashin zaizaiyar kasa.

Inda ya kara da cewa muhimmancin da bishiya take dashi bazai kirgu wanda daga ciki akwai tace iskar da mutane suke shaqa, da inganta lafiyar kasa, da inganta lafiyar Dan Adam da Kara yawan ruwan sama, da Kara yawan ruwan sama, da rage dumamar yanayi, da sauransu.

Ya kuma ce ya kamata a ce hukuma ta dauki tsatstsauran mataki akan masu saresu da kuma dawo da dokar da ta hana sare bishiyun, domin hukuntashi, da kuma kallafawa duk wani Dan kasa dasa bishiya 1 da kuma rainonta domin samun yawaitar su a gari da yanki dama kasa baki daya

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *