News
Makarantar Koyar Da Sana,oi Ta Fauza Tailoring Center Tayi Bikin Yaye Dalibinta 39.
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Makarantar koyar da matan aure da ’yan mata sana’o’i mai suna fauza tailoring center dake karamar Hukumar Fagge a jihar kano ta yaye dalibanta 39
Da take jawabi a wajen taron, Shugabar makarantar Fauziyya Muhammad wacce akewa lakabi da Fauziyya Sufi ta bayyana cewa a wannan makaranta suna koya wa mata sana’o’in dinki don tallafa wa matan aure da sauran mata su sami sana’o’in yi.
Mummunan Harin ‘Yan bindiga Ya Tilastawa Mazauna Garin Bassa Barin Gidajensu
Fauziyya Sufi ta cigaba da cewa tana Jin rashin dadin ta matukaga da gaske a wajen wasu kungiyoyin da gwamnati ke baiwa aikin koyawa mata Sana,oin dogaro dakai domin kuwa basa koyawa bil hakki da gaskiya yadda ya kamata
Ta ce wannan makaranta tana daya daga cikin ayyukan ta na ganin an tallafa wa al’umma su sami ayyukan yi, musamman matan aure.
Haka zalika an bude wannan makarantar ne tun a shekara 2002 da nufin inganta rayuwar Mata.
Ta yi kira ga al’umma da gwamnati da ta runga zakulo irin makaranmu domin gwamnati anaso itama ta dinga ayyukan alkhairi

Jaridar INDA RANKA ta ruwaito cewa taron ya du dana ne a jiya lahadi a harabar makarantar ta fauza dake unguwar kurna layin makaranta
Rahotanni na nuni da cewa makarantar Fauza tailoring center ta Saba yaye dalibai da dama a duk shekara inda a Wannan shekarar ta baiwa wasu daga cikin zakakuran marayu kyautar kekunan dinki har guda uku 3.

Taron ya Samu halartar manyan Baki da dama ciki harda jami,an tsaro masu milkin gargajiya ma masu inguwanni da manyan malamai

