Connect with us

News

Mummunan Harin ‘Yan bindiga Ya Tilastawa Mazauna Garin Bassa Barin Gidajensu 

Published

on

DAGA NUASIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA 

‘Yan bindiga sun tilastawa mazauna garin Bassa da ke noma a jihar Neja barin gidajensu sakamakon wani mummunan hari da ya yi sanadin mutuwar mutane 20.

Advertisement

Sanata mai wakiltar yankin Neja ta Gabas, Sani Musa, ya bayyana wannan mummunan labari a ranar Juma’ar da ta gabata yayin da yake tsokaci kan fille kai da kashe wasu matasa 20 ‘yan kabilar Bassa, da ke karamar hukumar Shiroro.

Aikin Hajji: Wata Hajiya daga Najeriya ta kashe kan ta a Madina

Sanatan ya bayyana cewa maharan sun fille kan wasu matasa 10 tare da kashe wasu mazauna garin 10 bisa zargin bijirewa bukatar ‘yan fashin na shiga kungiyarsu.

Advertisement

“Makonni uku kacal da suka wuce, wasu gungun ‘yan bindiga sun kai farmaki kauyen Kuchi, inda suka kashe jami’an tsaro bakwai tare da mutane kusan 150.

“Har zuwa wannan lokacin, duk al’ummar Kuchi sun kasance ba kowa. Wadannan hare-hare na baya-bayan nan na zuwa ne a lokacin da jama’a ke shirin komawa gona, wanda shi ne kawai sana’arsu,” inji shi.

Advertisement

Jaridar DAILY POST ta tattaro cewa an kai harin na baya-bayan nan a garin Bassa a ranar Alhamis. ‘Yan bindigar sun tara mutane kusan 20, da nufin shigar da su aikinsu. Yayin da 10 daga cikin matasan suka yi turjiya, an fille kawunansu. Sauran 10 kuma an harbe su.

Idan ba a manta ba, a watan Afrilu, kungiyar ta kai hari a unguwar Allawa, inda ta kashe mazauna garin tara bayan da ta yi galaba a kan sojojin da ke yankin.

Advertisement

Kokarin samun jin ta bakin mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, Wasiu Abiodun, ya ci tura har zuwa lokacin da aka bayar da rahoton.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending