News
Aikin Hajji: Wata Hajiya daga Najeriya ta kashe kan ta a Madina
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Wasu maniyyata guda biyu ƴan asalin jihar Kwara da ke aiwatar da aikin Hajjin bana a ƙasar Saudiyya daga jihar Kwara; Salihu Mohammed da Hawawu Mohammed, sun rasu a birnin Madina.
Sakataren zartarwa na Hukumar Alhazai ta Jihar Kwara, AbdulSalam AbdulKabir, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi.
Aikin Hajji: Karin Wani Mahajjacin Daga Jihar Kebbi Ya Rasu A Makkah
A cewar sa, yayin da Salihu Mohammed ya rasu a sashin kula da marasa lafiya na musamman na asibitin gwamnati da ke Madina bayan ya fara jinya cikin ƙanƙanin lokaci.
Wikki Times ta ruwaito cewa Hauwa’u Mohammed ta rasu, bayan abin da hukumomin ƙasar Saudiyya suka gudanar da bincike suka gano cewa ta kashe kanta ne, ta hanyar faɗowa, da gangan, daga saman benen masaukinta da ke Madina.
Hukumomin Saudiyya da na jihar Kwara sun bayyana faruwar lamarin a matsayin abin takaici gami da bakin ciki tare da mika sakon ta’aziyya ga iyalan mamatan.
-
News6 days ago
Ban Taɓa Nadamar Adawa Da Yunƙurin Obasanjo Na Wa’adin Mulki Karo Na Uku Ba — Atiku
-
News3 days ago
Wasu Kansiloli Na Zargin Ciyaman Da Daukar ‘Yan Daba Domin Kai Musu Hari A Kano
-
News6 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Ƙwato Na’urorin Solar 160 Da Darajarsu Ta Kai Kimanin Naira 59.2 A Kano
