Connect with us

News

Wasu fusatattun matasa sun cinnanwa ofishin hukumar zaɓe wuta a Jahar Binuwe

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

Advertisements
Advertisements

Rahotanni daga Shalkwatar hukumar zabe ta ƙasa INEC na tabbatar da aukuwar wannan danyen aiki da matasa masu zanga-zanga kan matsalar tsaro a garin Sankera da ke karamar hukumar Ukum na jihar ta Binuwe.

Advertisements

Matasan Sun fito wannan zanga-zanga ne bayan kisan wasu mutane 11 da wasu ɓata gari suka yi, abin da a cewar su ba shine karon farko ba da ‘yan ta’addan ke kai musu farmaki suna kashe musu jama’a a mahallan su.

Advertisements
Advertisements

Babban jami’in wayar da kan masu zabe na INEC a Abuja Sam Olumekun ya fadi cewa kwamishinan zabe na jihar Binuwe Farfesa Sam Egwu ya sanar da su cewa matasan sun yi wannan aika aika ne ga Ofishin na hukumar zaɓe na Sanƙara da misalin ƙarfe biyu na rana.

Tuni dai gwamnan jihar ta Binuwe Hyancinth Alia ya aikata dokar hana fita a ƙaramar hukumar ta Ukum saboda wannan zanga-zanga. dake gudana

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending